Lamari Ya Girma: Amnesty Intl Ta Shiga Dambarwar Yan Kwadago da Yan Sanda

Publish date: 2024-07-19

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Amnesty International ta yi kira na musamman ga hukumomi a Najeriya kan ƙungiyar kwadago.

Amnesty International ta ce bai kamata hukumomi su rika yin barazana ga yan kwadago a Najeriya domin dakile su ba.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Daraktan Amnesty Int'l a Najeriya, Isa Sanusi ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun gayyaci Joe Ajaero

Rundunar yan sandan Najeriya ta gayyaci shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero domin amsa tambayoyi.

Yan sanda sun ce ana zargin Joe Ajaero da hannu cikin wasu laifuffuka da suka hada da cin amanar kasa.

Martanin Amnesty Int'l ga yan sanda

Leadership ta wallafa cewa Daraktan Amnesty Int'l a Najeriya, Isa Sanusi ya ce sun nuna damuwa matuƙa kan yadda yan sanda suke barazana ga NLC.

Isa Sanusi ya ce ya kamata yan sanda su daina nuna barazana ga al'umma kuma su yarda cewa NLC tana da ikon kin yarda da tsare tsaren gwamnati.

Maganar kai hari ga Joe Ajaero

Haka zalika Amnesty Int'l ta kara da cewa an kai hari ga shugaban kwadago a shekarar da ta wuce wanda duk hakan na cikin barazana da ake yi wa NLC.

Kara karanta wannan

Daga karin kumallo, uwa da ƴaƴanta 3 sun rasu a wani yanayi mai ban tausayi

Amnesty Int'l ta kara da cewa a kwanakin baya yan sanda sun kai samame hedikwatar NLC inda suka tafi da wasu takardu wanda hakan bai dace ba.

Karin albashi: NLC ta yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa maimakin shugaban kungiyar kwadago na kasa ya magantu kan yadda aka samun jinkirin biyan mafi ƙarancin albashi.

Farfesa Theophilus Ndubuaku ya ce akwai abubuwa da dama wanda dole sai an kammala su kafin a fara biyan sabon albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYZ0fpVmmKamlajBunnIp6ulZaSWerS0yKCYZpyRoq%2BivtaaqWaxkaN6rMPAnZigp12Zrm7FwKdkrJmema5uwMBmsKJll5a%2FqK3DomY%3D